A duk lokacin da aka yi magana kan kasuwar cryptocurrency, mutane da dama kan fi mayar da hankali ne kan farashin Bitcoin ko kuma ko Altcoins za su tashi. Amma babbar tambayar da ta fi muhimmanci ita ce: Yaya kasuwar crypto za ta kasance bayan shekaru 20 masu zuwa?
Duk da cewa babu wanda zai iya hango makoma da tabbacin kashi 100%, akwai alamomi masu ƙarfi da ke nuna cewa duniya na tafiya zuwa wani sabon tsarin tattalin arziki da blockchain zai yiwa kaka gida.
1. Crypto Zaibi Sahun Intanet
Shekaru ashirin da suka gabata, mutane da yawa ba su fahimci muhimmancin intanet ba. A yau kuwa, rayuwa ta zama kusan ba za ta yiwu ba ba tare da ita ba.
Haka ma crypto na iya bi. Maimakon mutane su rika cewa "Ina amfani da crypto", za su rika amfani da ayyukan da blockchain ke gudanarwa ba tare da sun ma sani ba.
Biyan kuɗi, aika kuɗi tsakanin ƙasashe, mallakar kadarori, da kasuwancin hannayen jari na iya gudana ta blockchain cikin sauri da ƙarancin kuɗi.
2. Tasirin Tokenization
Daya daga cikin manyan sauye-sauyen da ake tsammani shi ne Tokenization, wato mayar da kadarorin duniya zuwa dijital.
Ana sa ran abubuwa kamar:
Gidaje
Filaye
Zinariya
Hannayen jari
Takardun gwamnati (Bonds)
Kayayyakin more rayuwa
za su kasance a blockchain.
Wannan zai ba gama garin mutane damar mallakar wani kaso na manyan kadarori cikin sauƙi, ba tare da sun kasance masu arziki ba. Bankuna da manyan cibiyoyin kuɗi sun riga sun fara gwada irin wannan fasaha.
3. Bankuna Zasuyi Amanna Da Crypto
A farkon shekarun crypto, bankuna da dama sun yi adawa da shi.
Amma yanzu abubuwa sun canza.
Manyan cibiyoyin kuɗi suna zuba biliyoyin daloli a harkar crypto, suna gina kayayyakin tokenization, custody, da sabbin hanyoyin kasuwanci. Wannan yana nuna cewa ana kallon crypto a matsayin wani bangare na tsarin kuɗi na gaba, ba wai wata fasaha ta wucin gadi ba.
4. Gwamnatoci Za Su Ƙirƙiri Kuɗin Dijital Nasu (CBDC)
Kasashe da dama suna bincike ko gwajin Central Bank Digital Currency (CBDC).
Amma wannan ba yana nufin Bitcoin ko Ethereum za su bace ba.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Masana na ganin CBDCs da cryptocurrencies za su iya rayuwa tare, kowanne yana da rawar da yake takawa.
5. Dokokin Gudanarwa
Babban ƙalubalen crypto shekaru da dama shi ne rashin cikakkun dokoki.
A cikin shekaru masu zuwa ana sa ran ƙasashe za su samar da ƙa'idoji masu kyau waɗanda za su kare masu zuba jari tare da bai wa kamfanoni damar haɓaka sabbin fasahohi.
Wannan na iya kara jawo hankalin manyan masu hannu da shuni zuwa kasuwar.
6. Kyakkyawar Alaƙar Blockchain Da AI
Artificial Intelligence (AI) na ci gaba da bunƙasa.
Blockchain kuma na samar da gaskiya da tsaro.
Haɗin waɗannan fasahohi zai iya samar da sabbin kasuwanci, sabbin ayyuka da kuma tsarin tattalin arziki da ba a taɓa gani ba.
8. Bitcoin Zai Ci Gaba Da Kasancewa "Digital Gold"
Duk da tashi da faduwar farashi, Bitcoin zai ci gaba da kasancewa mafi girman cryptocurrency.
Idan tarihi ya ci gaba da maimaita kansa, mutane da dama za su rika kallonsa a matsayin hanyar adana dukiya, kamar yadda ake kallon zinariya a yau.
Kalubalen Da Har Yanzu Suke Gaban Crypto
Ba komai zai kasance cikin sauƙi ba.
Har yanzu akwai ƙalubale kamar:
Hare-haren masu kutse.
Zamba da rug pull.
Volatility.
Matsalolin dokoki a wasu ƙasashe.
Gasa tsakanin blockchain daban-daban.
Waɗannan abubuwa za su ci gaba da zama ƙalubale, amma tarihin fasaha ya nuna cewa sababbin hanyoyi kan magance irin waɗannan matsaloli a hankali.
Kasuwar crypto bayan shekaru 20 ba za ta yi kama da yadda take a yau ba. Wataƙila ba za mu rika magana kan "crypto" kaɗai ba, domin blockchain zai kasance cikin bankuna, kasuwanni, gwamnati, inshora, gidaje, hannayen jari, da kusan dukkan tsarin kuɗi.
Abin da muke gani a yau na iya zama farkon wani babban sauyi ne kawai.
Tambaya: Kana ganin Bitcoin da sauran cryptocurrencies za su zama ginshiƙin tattalin arzikin duniya nan da shekaru 20, ko kuwa za su kasance kayan saka hannun jari kawai? Menene ra'ayin ka?