Kasuwar hada-hadar crypto ta kasar Koriya ta Kudu ta dade tana matsayin daya daga cikin manyan ginshikai da ke turawa da kuma ruruta wutar yaΙ—uwar kasuwancin crypto a duniya. Rubu-bi da 'yan kasar suka yi wa harkar, wanda aka fi sani da "Kimchi Premium," ya nuna Ζ™arfin kishirwar crypto a yankin. Sai dai, a halin yanzu, crypton na fuskantar barazana: Dillalai (Traders) na Koriya ta Kudu suna janye kudadensu tare da barin kasuwar.

Wannan ba matsala ce ta Koriya kadai ba; gargadi ne mai karfi ga daukacin duniyar crypto musamman (Exchanges). Idan har ba su mayar da hankali ba, wannan guguwar zata yi awon gaba farin cikin kasuwar su.


Me Yasa Suke Fecewa Daga Kasuwar?

Wadannan dalilai da zamu kawo zai zama ishara ga sauran kasuwannin crypto, ya zama lallai su sake Ι—amara 


1. Tsauraran Dokoki (Regulatory Squeeze)

Gwamnatin Koriya ta Kudu ta tsaurara matakan tace dandamalan hada-hadar crypto na cikin gida. Sabbin dokoki domin kare dukiyar yan Ζ™asa masu zuba jari sun takaita irin nau'ikan coins da za'a iya (listings), sannan sun kara sanya ido kan harkar harajin crypto. Wannan takunkumi ya rage wa Ζ΄an crypton karsashi da 'yancin yin kasuwanci yadda suka saba.


2. Sauyin Ra'ayi Zuwa Kasuwar Stock 

Maimakon jiran tsawon lokaci a kasuwar crypto da ke cike da fadi-tashi, yan crypton da dama suna karkata akalarsu zuwa kasuwannin hannun jari na gargajiya, musamman kasuwar Amurka (U.S. Tech Stocks). Tabbaci da kuma damar samun riba mai dorewa a can yana jan hankalin su fiye da hadarin da ke cikin crypto a halin yanzu.


3. "Ƙosawar Kasuwa" (Market Fatigue)

Bayan shafe lokaci mai tsawo ana fuskantar yanayin "Bear Market" da kuma rashin tabbas, dillalai da dama sun koka da yadda portfolio dinsu yake jin jiki. Rashin samun labarai masu dadi (bullish catalysts) ya sanya da yawa daga cikinsu sun gwammace su fita domin tsira da abunda kasuwar ta rage musu.


Me Yasa Yake da Muhimmanci Ga Kasuwannin Crypto? 

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Raguwar Kudaden Shiga Daga Haraji (Trading Fees): Koriya na daya daga cikin kasashen da ke samar da mafi yawan kudaden mu'amala (volume). Idan babu su, kudaden shiga na exchanges zai ragu sosai.

Ƙarancin Liquidity (Liquidity Drop): Ficewar manyan traders na nufin samun karancin masu saye da sayarwa a kasuwa. Wannan yana sa farashin abubuwa yin kasa cikin sauri da zarar an sami 'yar matsala.

Alamar Abin da Ke Tafe A Sauran Kasashe: Abin da ke faruwa a Koriya yanzu zai iya faruwa a Amurka, Turai, ko sauran sassan Asiya idan har ba a samar da mafita ba.


Wane Mataki Yakamata A Ɗauka?

Tsauraran Dokoki: Shiga tsarin bada lasisi na gaskiya da nuna gaskiya (Transparency) don dawo da amana.

Zaburaswa: Samar da sabbin kayayyakki (Innovations) kamar dabarun AI trading da tsare-tsaren rage asara.

Wayar Da Kai: Maida hankali kan ilmantar da mutane (Crypto Education) da samar da rangwame na musamman ga tsofaffin yan kasuwar.

Yayin da dillalan Koriya ke ja da baya, wannan babban darasi ne ga kasashen da ke tasowa a fannin crypto, kamar kasashen Afirka. Kasuwar crypto tana bukatar juriya, ilimi, da kuma bin diddigin manufofin gwamnati.

Ga dandamalan siye da siyarwar crypto na duniya, lokacin nuna halin ko-in-kula ya wuce. Ficewar yan crypton Koriya kararrawa ce mai karfiβ€”ko dai ku sauya tsari don dacewa da bukatun investors, ko kuma ku tsaya kallon ruwa kwaΙ—o yayi muku Ζ™afa.


Wadanne irin kalubale ne kuke fuskanta a yankunan ku?