A duniyar kasuwancin Crypto, akwai wata tsohuwar magana da kusan kowa ya sani: "Buy the rumor, sell the news" (Sayi jita-jita, siyar da labari). Amma ga sababbin βyan kasuwa, akwai wani abu guda daya da ya fi komai daure kai: Invisible Delayβwato jinkirin da ake samu tsakanin lokacin da labari ya fito da kuma lokacin da farashi zai yi martani.
Shin ka taba ganin inda aka fadi wani babban labari mai dadi game da wani Coin, amma maimakon farashin ya tashi, sai ka ga yana ta faman tafiyar hawainiya ko ma ya fadi? To, ba kai kadai ba ne. Ga dalilan da suke sa hakan na faruwa:
1. Tasirin "Smart Money" (Wayayyun Masu Kudi)
Kafin labari ya isa gare ka a matsayinka na dan kasuwa na gida (Retail Trader), tuni manyan kifayen kasuwa (Whales) sun dade da sanin sa. Suna amfani da kwarewa da naβurori masu saurin gaske wajen siye tun kafin labarin ya fito fili. Lokacin da kai ka karanta labarin a Twitter ko Telegram, su kuma a lokacin ne suke kwashe ribar su. Wannan jinkirin shi ne yake sa ka ga farashi ya ki tashi yadda kake zato.
2. Matsalar Tace Labari (Market Absorption)
Kasuwar Crypto ba mutum daya ba ne; hadaka ce ta miliyoyin mutane masu ra'ayi daban-daban. Lokacin da labari ya fito, kasuwa na bukatar lokaci ta tantance:
Shin labarin gaskiya ne?
Shin tasirin sa na dan lokaci ne ko na din-din-din?
Wane mataki ya kamata a dauka?
Wannan lokacin nazarin shi ne yake haifar da wannan shiru-shirun da kake gani kafin ka ga farashi ya dauki wata hanya.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
3. Karancin Liquidity (Liquidity Constraints)
Wani lokaci, labarin yana da dadi kwarai, amma babu isassun kudade (liquidity) da zasu tura farashin sama nan take. Idan masu sayarwa (Sellers) suka ki saki, ko kuma masu saya (Buyers) basu da kwarin gwiwar shiga da kudi mai yawa a lokacin, farashin zai tsaya ne cirko-cirko har sai an samu kwararar sabbin kudade.
4. Rawar Da "Bots" Suke Takawa
A yau, kusan kashi 70% na kasuwancin crypto ana yin sa ne ta amfani da Algorithms da Trading Bots. Wadannan naβurori suna karanta labarai cikin sakan daya. Idan bot ya ga labarin bai cika ka'idojin da aka sa masa ba, ba zai saya ba. Wannan na iya sa labari mai dadi ya bayyana, amma tunda na'urori basu motsa ba, farashi ba zai tashi ba.
Ta Yaya Zaka Kare Kanka Daga Wannan Jinkirin?
Kada Ka Bi Zuga (FOMO): Idan ka ga labari ya dade da fitowa (misali awa biyu ko uku), kar ka riga ka daka tsalle ka shiga kasuwar da gudu. WataΖila tasirin sa ya riga ya wuce.
Kalli Taswirar Farashi (Technical Analysis): Kar ka dogara da labari kadai. Duba shin taswirar (chart) tana goyon bayan labarin?
Kasance Mai Hakuri: Wani lokaci farashi baya tashi a ranar da labari ya fito, sai bayan kwanaki biyu lokacin da kowa ya riga ya amince da labarin.
Kasuwar Crypto ba tseren gudu ba ne na sakan daya; tseren dogon nishadi ne (marathon). Fahimtar wannan "Invisible Delay" zai baka damar natsuwa wajen yanke shawara, maimakon ka zama abincin manyan kifi.
Shin kai ma ka taba shiga kasuwa saboda wani labari amma sai ka ga akasin abin da kake fata ya faru? Fada mana experience Ιinka a comment!