Kusan kowane dan crypto ya taba shiga wannan zulumin: Ka zauna ka shafe awanni kana nazarin chart, ka fitar da layukan Support da Resistance dinka daidai. Farashi ya matso, ya daki layinka, sannan ya fasa shi da karfi (Breakout). Nan take ka danna shiga kasuwa domin kada a barku a baya, amma sai farashin ya juya daidai inda ka shiga, ya tafi da kudadenka.

Shin kasuwar ce ke fada da kai? Ko kuma kai baka iya bane?

A'a, babu ko daya. Wannan shi ake kira Liquidity Hunt (Farautar Kudade) ko kuma Fakeout. Labari mai dadi shi ne, idan ka gane yadda manyan dillalai (Whales) ke amfani da wannan dabarar, zaka daina fada wa tarkonsu, kai ma zaka iya juya abun ya dawo maka da riba.


Menene Ke Faruwa A Bayan Fage?

Kasuwar crypto ba ta tafiya haka kawai; tana tafiya ne ta inda kudi yake. Domin manyan Whales su sami damar sayen ko sayar da jimillar crypto ba tare da sun tsoratar da kasuwa ba, suna bukatar gano inda kudaden kananan ’yan kasuwa (Retail Traders) suke a ajiye.

A ina ne wadannan kudaden suke? Suna nan makale a wajaje guda biyu:

Stop Losses: Da ke daf da saman Resistance ko karkashin Support.

Breakout Orders: Na mutanen da ke jiran farashi ya fasa level kawai su shiga.

Whales din nan suna tura farashin da gangan domin ya daki wadannan odar, su kwashe kudaden (Liquidity), sannan su juya kasuwar ta nufi ainihin inda suke so tun farko.


Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Yadda Zaka Gane Breakout Na Gaske Da Na Bogi

Kafin ka garzaya danna "Buy" ko "Sell", kula da wadannan abubuwa guda biyu:

Girman Candlestick: Idan breakout din na gaske ne, candle din yana rufewa a wajen level din da karfi. Idan na bogi ne (Fakeout), zaka ga candle din ya fita sannan ya dawo ciki da sauri, ya bar dogon jela (wick) a sama ko kasa.

Volume (Adadin Ciniki): Breakout na gaske yana tafiya ne da babban Volume. Idan kaga farashi ya fasa kofa amma Volume din yana kasa, tabbas tarko ne a wurin.


Dabarar Kauce Wa Wannan Tarkon

Maimakon ka zama abincin Whales, ga hanyoyi biyu da zaka kare kanka:

1. Jira Tabbaci (Retest): Kar ka shiga kasuwa a daren farko da kaga an fasa layinka. Jira farashin ya dawo ya sake taba wannan layin (Retest). Idan ya kasa komawa ciki kuma ya juya da karfi, to anan ne zaka shiga cikin kwanciyar hankali.

2. Juya Tarkon Ya Zama Riba: Idan kaga farashi ya fasa Resistance amma ya gaza rufewa a samaβ€”maimakon haka ya bar dogon jela kuma ya dawo karkashin layinβ€”wannan ita ce damarka ta yin Short. Domin kasuwar ta nuna maka cewa babu masu siye na gaske a saman, Whales sun riga sun gama aikinsu.

Kasuwar crypto tana bukatar hakuri da natsuwa. Daga yau, idan kaga farashi ya fasa level dinka, bar shi ya huta, ka binciki Volume dinsa kafin ka yanke hukunci.