Afrika ita ce nahiyar da bangaren internet da harkar digital suke girma cikin sauri fiye da ko ina a duniya. Amfani da internet ta waya yana karuwa sosai. Biyan kudi ta waya da online yana karuwa sosai. Online shopping, fintech, da online banking yanzu sun zama ruwan dare daga Lagos zuwa Nairobi zuwa Accra. Miliyoyin mutane da basu taba samun bank account ba yanzu suna tura kudi da karbar kudi online kullum.
Kuma masu damfarar internet sun san hakan.
Masu Hari Suna Karuwa Fiye da Tsaron Da Ake Da Shi
Yayin da karin mutane a Afrika suke shiga online, karin mutane suna zama targets ga cybercriminals alhali systems din da ake amfani dasu wajen kare mutane suna baya sosai. Yawancin businesses a Afrika basu da isasshen tsaron cybersecurity. Government systems da yawa tsofaffi ne kuma masu saukin shiga. Yawancin mutane kuma ba su san basic hanyoyin kare kansu online ba.
Sakamakon haka shi ne Afrika tana kara zama target ga local da international cybercriminal groups. Mobile money fraud, satar SIM, phishing attacks, ransomware da ke kai hari kan businesses, da satar bayanan mutane duk suna karuwa sosai a fadin nahiyar.

Karancin Experts Babbar Dama Ce

Ga daya bangaren labarin kuma. Afrika tana fama da karancin mutanen da suka kware a cybersecurity kuma bukatarsu tana kara girma duk shekara. Companies, banks, governments, da NGOs suna neman mutanen da suka san yadda ake kare systems na digital. Kuma suna shirye su biya kudi masu yawa saboda wannan skill din.

Cybersecurity analyst a Nigeria zai iya samun daga ₦500,000 har sama da ₦2 million a wata yana aiki remotely ga international companies. Mutanen da suka samu certifications a ethical hacking, cloud security, ko incident response yanzu ana daukarsu aiki daga ko ina a duniya suna aiki daga laptops dinsu daga gida.

Daga Ina Za Ka Fara?

Ba sai kana da computer science degree ba kafin ka shiga cybersecurity. Akwai free da affordable platforms kamar Cybrary, TryHackMe, da Coursera da suke koyarwa daga farko har zuwa mataki mai kyau. Certifications kamar CompTIA Security+, Certified Ethical Hacker (CEH), da Google Cybersecurity Certificate ana gane su a duniya kuma ana iya kammala su cikin watanni kadan.

Bottom Line

Digital economy a Afrika ana gina shi ne yanzu. Mutanen da suka koyi yadda za su kare shi za su samu aikin yi da opportunities na dogon lokaci.