A shekarar 2024, wani finance employee a Hong Kong ya tura dala miliyan 25 zuwa hannun criminals bayan ya shiga wani video call da yake tunanin CEO na company dinsu ne tare da wasu colleagues. Amma gaskiyar ita ce duk mutanen da suke cikin wannan call din deepfake ne. AI-generated video replicas masu matukar kama dana gaske har babu wanda yayi shakka sai bayan kudin ya bace. Wannan ba science fiction ba ne. Wannan yana faruwa a yanzu.

Menene Deepfakes?

Deepfakes su ne AI-generated videos, images, ko audio recordings da suke sa mutum na bogi ya bayyana kamar yana magana ko yin wani abu da bai taba yi ba. Technology din yaci gaba sosai har yanzu ana iya kirkirar convincing deepfake na kowa ta amfani da hotuna ko video clips kadan da aka samu a online cikin mintuna kaΙ—an ba tare da bukatar technical expertise ba.

An taba yin deepfake na political leaders suna bada speeches daba su taba yi ba. An saka celebrities cikin explicit videos ba tare da izininsu ba. Har ma ordinary people anyi clone faces dinsu domin aikata zamba kan iyalansu da mutanen da suka sani.

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Matsalar ita ce, yayin da AI ke kara yin wayo, yana kara wahalar da mutane su bambance tsakanin gaskiya da karya. Video da kake gani da idanunka ba yana nufin gaskiya ba ne kuma Voice da kaji da kunnuwanka ba lallai ya zama na mutumin gaske ba. Wannan yana bude kofar scams, manipulation, blackmail, da fake news a wani mataki da duniya ba ta taba gani ba.

A yanzu, ba tambayar β€œshin za a iya yin deepfake?” ba ne. Tambayar ita ce: β€œTa yaya zamu san mene yake gaskiya?”