Ba a fitar da manya manyan sanarwar korar ma’aikata. Babu zanga-zanga a wajen office buildings. Sauyin yana faruwa ne a hankali daya bayan daya, role daya bayan daya kuma yawancin mutane ba zasu gane ba sai lokacin da ya riga ya makara.

Artificial intelligence wato AI baya fara zuwa kan CEO. Yana zuwa ne kan intern. Junior writer. Customer service rep. Data entry clerk. Graphic design assistant. Entry-level analyst. Wadannan su ne ayyukan da miliyoyin matasa musamman a Afrika suka saba amfani dasu domin fara gina rayuwarsu. Kuma suna bacewa da sauri fiye da yadda kowanne generation ya taba tunani.

Abubuwan Da Tuni Suka Fara Bacewa

Customer service yana daya daga cikin abubuwan farko da suka fara faduwa. Kamfanoni a duniya sun maye gurbin human agents da AI chatbots da suke aiki awa 24 ba tare da gajiya ba, basa neman karin albashi, kuma suna iya handling dubban conversations a lokaci guda. Bambancin quality tsakanin mutum da AI yana kara raguwa sosai.

Basic content writing, product descriptions, simple articles, social media captions yanzu AI keyi a mafi yawan lokuta. kamfanoni da a da suke daukar teams na junior writers yanzu suna amfani da AI tools domin samar da content iri daya cikin karamin lokaci da karamin kudi.

Data entry, basic accounting, simple legal document drafting, appointment scheduling, basic graphic design, har ma da junior coding tasks yanzu AI tools sunayi cikin sauri kuma da rahusa fiye da mutane.

Babbar Matsalar Da Ke Boye a Ciki

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Entry-level jobs ba albashi kawai suke bayarwa ba. Wurin koyo ne. Kana shiga matsayin junior, kana yin mistakes, ana mentoring dinka, sannan ka girma. AI yanzu yana rage wannan pipeline din gaba daya. Matasa suna fafatawa ne kan karancin starting positions, wanda ke nufin karancin damar samun experience da ake bukata domin kaiwa senior roles.

Wannan yana haifar da wata matsala mai hadari generation mai ilimi amma babu inda zai fara.

Me Ya Kamata A Yi?

Amsa ba tsoro ba ce amsar ita ce canzawa. Ayyukan da AI ba zai iya maye gurbinsu cikin sauki ba sune wadanda suke bukatar human judgment, creativity, emotional intelligence, da complex decision-making. Ka koyi skills da suke sama da entry level project management, AI tool operation, cybersecurity, data analysis, digital marketing strategy. Ka zama mutumin da yake sarrafa AI, ba wanda AI yake maye gurbinsa ba.

Entry-level job kamar yadda muka sani yana canzawa. Hanya daya tilo ta gaba ita ce ka canzawa tare da shi.